10 Janairu 2022 - 14:57
​ECOWAS Na Taro Kan Mali A Wannan Lahadin

Shugabanni da gwamnatocin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika na halartar wani taro a birnin Accra na kasar Ghana mai manufar tattauna halin da ke ciki a Mali.

Ana zaton ko taron zai dauki matakin kakabawa hukumomin sojin Malin takunkumi mai tsauri domin tilasta masu dawowa kan madaidaiciyar hanya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Har illah yau akwai kuma wata haduwa ta shugabannin kungiyar kasashe masu amfani da kudin bai daya na CFA, amma ban da Mali wacce aka dakatar daga kungiyar sabod ajuyin mulkin sojoji.

Kafin hakan dai gwamnatin sojin Mali ta ce ta mika sabon jadawali ga kungiyar ECOWAS wanda ya kunshi lokacin da mulki zai koma hannun farar hula.

Ministan harkokin waje, Abdoulaye Diop ne ya mika wa shugaban rikon na kungiyar ta ECOWAS, kuma shugaban Ghana Nana Akufo-Addo, sai dai ba a bayyana ainahin lokacin da za a mika mulkin ba.

Kungiyar ECOWAS dai ta yi watsi da wa’adin shekaru biyar da sojoji suka bayar a baya kan cewa shi zasu mika mulki ga farar hula.

342/